Isa ga babban shafi
Syria- Tarayyar Larabawa

Wakilan kungiyar Larabawa zasu kai ziyara Syria

A yau ne ake sa ran wakilan kungiyar larabawa zasu kai ziyara kasar Syria karkashin yarjejeniyar kokarin kawo karhen jubar da jinin da ake yi a cikin kasar inda Majalisar Dinkin Duniya tace mutane 5,000 ne aka kashe tun fara zanga-zangar adawa da Bashar al Assad.

Daruruwan masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad
Daruruwan masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad Reuters
Talla

Kasashen Yammacin duniya na bukatar daukar matsayin bai daya kan hukumomin kasar, yayin da shugaba Bashar al Assad ke zargin ‘Yan bindiga da kai harin.

A yau alhamis ne kasar Amurka ta yi kiran ‘yan kasar fice daga Syria tare da bada gargadin kauracewa kasar ga masu neman zuwa.

Tuni dai kasar Rasha ta gabatar da wani daftari da ke la’antar rikcin Syria a zauren kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Wakilan kasashen Larabawa kimanin 30 ne tare da ‘Yan Jarida ake sa ran zasu kai ziyara kasar Syria domin diba halin da ake ciki a kasar kafin ziyarar manyan wakilan kasashen a ranar Lahad da ake sa ran zasu kwashe tsawon wata daya domin diba yadda za’a sasantawa tsakanin Gwamnati da ‘Yan adawa.

Wakilan kasashen zasu nemi kawo karshen rikicin tare da neman bukatar ganin dakarun kasar sun kauracewa wuraren gudanar da zanga-zanga.

An dade ana neman amincewar kasar Syria game da ziyarar wakilan, amma sai a ranar Litinin ne kasar ta amince da ziyarar. Amma Ministan harakokin wajen kasar yace wakilan zasu samu kariya da kulawar gwamnati.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.