Ana ci gaba da rikici a Syria bayan ziyarar masu sa ido
Tawagar Kungiyar kasashen Labarawa na ci gaba da sa ido a sassan kasar Syria, yayin da ake cigaba da tashin hankali inda ‘Yan rajin kare Hakkin Bil adama ke tabbatar da mutuwar mutane 10 sanadiyar dauki ba dadi tsakanin Masu zanga-zanga da Jami’an tsaro.
Wallafawa ranar:
Amma shugaban tawagar Larabawan ya musanta rahotannin da kungiyoyin ke yadawa, inda yake cewa, shi ya zuwa yanzu bai ga wani abu mai tada hankali ba.
A bangare daya kuma, shugaba Bashar al Assad ya saki mutane 755 da aka kama a lokacin tashe tashen hankulan.
Waikilan kungiyar zasu kai ziyara birnin Hama da yankin arewa masu gabacin Idib da kudancin birnin Deraa inda aka fara gudanar da zanga-zangar a kasar.
‘Yan rajin kare hakkin Bil’adama sun ce akalla mutane 40 sun mutu cikin kwanaki biyu da fara ziyarar wakilan kungiyar Larabawa a cikin kasar.
Kungiyar kare hakkin bil’adata mai sa ido a kasar Syria tace an kashe wasu Soji hudu da suka canza sheka a birnin Deraa da kuma fararen hula da aka kashe a gundumar Amr a birnin Homs da kuma yankin Hama da Aleppo.
Shugaban wakilan kungiyar Janar Mustafa al-Dabi, dan kasar Sudan ya shaidawa kamfanin Dillacin Labaran Reuters cewa al’amurra sun fara sauyawa a kasar amma kuma basu ga wani abun tashin hankali ba kawo yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu