Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

An bayyana Kim Jong-un matsayin sabon shugaban Koriya ta Arewa

A kasar Koriya ta Arewa an bayyana Kim Jong-un dan autan Kim Jong-il matsayin sabon shugaban kasa bayan kammala Jana’izar mahaifin shi wanda ya mutu saman kujerar shugabancin kasar.A yau Alhamis dubun dubatar ‘yan kasar ne suka gudanar da bukin juyayin mutuwar Kim Jong-il tare da bayyana dan autansa matsayin sabon shugaban kasa.

Sabon shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un
Sabon shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un REUTERS / KCNA
Talla

A lokacin da Kim Yong-Nam shugaban gwamnatin kasar ke gabatar da jawabi gaban daruruwan mutane a dandalin wintry a Pyongyang ya yi jinjina ga tsohon shugaban wajen samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a kasar.

Dubban mutane ne suka halarci jana’izar da aka gudanar jiya laraba, a Dandalin Pyongyang, tare da sabon shugaban kasar, Kim Jong-Un.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.