Isa ga babban shafi
Syria

Syria ta yi watsi da bukatar kungiyar Larabawa

Gwamnatin Syria ta yi watsi da bukatar kungiyar kasashen Larabawa dangane da neman shugaban kasar Bashar Assad ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa domin samar da gwamnatin hadin gwiwa.A ranar Lahadi ne Kungiyar Kasashen Larabawa ta bukaci shugaba Bashar al Assad ya mika ragamar mulkin kasar ga mataimakinsa, domin kafa Gwamnatin hadin kai.

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad REUTERS/SANA/Handout
Talla

Bayan taron da kungiyar ta gudanar a birnin Alkahira na Masar, ta hannun shugabanta, kuma Fira Ministan Qatar, Sheikh Hamad bin Jassim al Thani, kungiyar ta bukaci mataimakin shugaban kasa kafa Gwamnatin hadin kai cikin watanni biyu.

Sai dai gwamnatin Syria tace kungiyar ya dace ta mayar da hankali wajen yaki da tallafawa ta’addanci ba rikicin wata kasa ba.

Tun a ranar 26 ga watan Disemba ne wakilan kasashen larabawa suka kai ziyara kasar Syria domin diba halin da ake ciki a kasar, sai dai sun fuskanci suka wajen rashin aiwata wani abun azo a gani da zai kawo karshen zubar da jini a Syria.

Tuni dai kasar saudiyya ta janye jekadunta da ke aikin sa ido a Syria bisa rashin mutunta wakilan da gwamnatin Syria ta yi.

Yanzu haka kuma kungiyar Larabawa ta cim ma yarjejeniyar sake tura wasu jekadunta domin neman sasantawa da gwamnatin Assad.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.