Isa ga babban shafi
Pakistan

Wani bene ya rubta da mutane a Pakistan

Wani yaron dan shekaru 12 ya mutu, daruruwan mutane da dama da suka hada da mata da yara ne suka fada a tarko bayan da ginin bene ya rubta dasu a birnin Lahore na kasar Pakistan.Wasu shaidar gani da ido sunce, akalla mutane 150 ke aiki a masana’antar da ginin ya rubta, kuma suna zaton tulun iskar gas ne ya fashe, abinda ya sa ginin rushewa.

Wasu mata suna juyayin mutuwar wani dan uwansu Chaudhry Mohammad Gulab  mai shekaru 62 wanda ya mutu sanadiyar ciwon zuciya a birnin Lahore
Wasu mata suna juyayin mutuwar wani dan uwansu Chaudhry Mohammad Gulab mai shekaru 62 wanda ya mutu sanadiyar ciwon zuciya a birnin Lahore REUTERS/Mohsin Raza
Talla

‘Yan sandan kasar sun ce kimanin mutane 40 ne ke cikin benen hawa uku lokacin da al’amarin ya auku.

Wani wakilin Kamfanin Dillacin labaran AFP yace akwai mata da kananan yara da ya tabbatar da idonsa ana fitowa dasu jina-jina daga cikin benen.

‘Yan sandan sun tabbatar da mutuwar wani yaro karami dan shekaru 12 na haihuwa kuma 'Yan Sandan sunce mata tara ne suka jikkata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.