Isa ga babban shafi
Pakistan

Pakistan ta yi fushi kan rahoton NATO

KASAR Pakistan ta bayyana bacin ranta kan wani rahotan asiri na kungiyar kawancen tsaro ta NATO, wanda ya zargi jami’an tsaron kasar da taimakawa Yan kungiyar Taliban a kasar Afghanistan. Rahotan wanda aka tsegunta wa manema labarai, yace Jami’an tsaron ISI na Pakistan na taimakawa Taliban a kasar Afghanistan, kamar yadda wasu shaidu 4,000 suka bada bahasi, yayin da ake yi musu tambayoyi.Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan, Abdul Basit, yayi watsi da zargin, inda yake cewa su ba sa sanya hannu kan harkokin cikin gidan Afghanistan. Wannan rahoto ya dada fito da zargin da Amurka da kasashen Yammacin duniya ke yiwa Pakistan, na jan kafa wajen yaki da ta’addanci, kamar yadda mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka, Captain John Kirby ya bayyana.Rahoton yace, Pakistan ta san inda shugabanin kungiyar Taliban suke, amma taki bada hadin kai, wajen sanar da kungiyar NATO domin kai musu hari.Maimagana da yawun kungiyar NATO, Lt Col Jimmie Cummings, yaki cewa komai kan lamarin, inda yace rahotan na asiri ne, saboda haka bashi da hurumin Magana akai. 

Prime Ministan Pakisan Yusuf Raza Gilani
Prime Ministan Pakisan Yusuf Raza Gilani REUTERS/Omar Sobhani
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.