Isa ga babban shafi
Amurka-Pakistan

Pakistan ta katse hulda tsakaninta da Amurka

Fira Minitan kasar Pakistan yace Pakistan zata katse duk wata huldar kasuwanci tsakaninta da Amurka bayan da dakarun NATO suka kai wani wani da ya yi sanadiyar mutuwar Sojojin Pakistan 24.

Wasu Mambobin Jam'iyyar Musulunci ta  Jamaat-e-Islami Rike ta wata Tuta suna zanga-zangar adawa da harin NATO a yankin Charsadda arewa maso yammacin Pakistan
Wasu Mambobin Jam'iyyar Musulunci ta Jamaat-e-Islami Rike ta wata Tuta suna zanga-zangar adawa da harin NATO a yankin Charsadda arewa maso yammacin Pakistan Reuters路透社
Talla

Sai dai kuma mai Magana da yawun fadar Gwamnatin Amurka Jay Carney, yace kashe Sojin Pakistan a harin da dakarun NATO suka kai ranar Assabar bai dace ya dama dangantaka tsakanin kasashen biyu ba.

A cewarsa, Shugaba Obama ya tausayawa wadanda suka rasa rayukansu, kuma sun dauki wannan al’amari ba da wasa ba. Yace dangantaka tsakanin kasashen biyu na nan daram, kuma zata dore.

Yana mai cewa kyakkyawar dangantaka na da muhimmanci ga Amurka, musamman a yakin da kasar Amurka ke yi da ta’addanci.

Kasar Pakistan dai tace daga yanzu babu sauran Hulda tsakaninta da Amurka bisa halaka mata dakarunta ba tare da wani dalili ba.

Yanzu haka Kungiyar NATO da Amurka suna kokarin bin hanyoyin dabarun lallashin Pakistan kasancewar Pakistan ta toshe hanyar da suke kai wa ga Dakarunsu dubu 140 dake Afghanistan.

A yanzu haka kuma kasar Rusha ta nemi ayi cikakken bincike akan lamarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.