Isa ga babban shafi
Syria

Kungiyar kasashen Larabawa tana taro kan Syria

Yau Lahadi Ministocin harkokin wajen kungiyar Kasashen Larabawa zasu tattauna mataki na gaba kan rikicin kasar Syria, bayan Kwamitin Sulhun MDD ya kasa cimma matsaya akai cikin makon jiya.Taron na birnin Alkahira na kasar Masar, ana saran zai duba yuwuwar tura masu saka ido na hadin gwiwa tsakanin kasashen na Larabawa da MDD.

REUTERS/Handout
Talla

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun bayyana mutuwar akalla mutane 45 cikin kasar ta Syria jiya Asabar, yayin karawa tsakanin masu zanga zanga da dakarun gwamnatin Bashar al-Assad.

Yanzu haka ana samun masu ikirarin Jahadi da makamai suna tsallakawa daga Iraki zuwa Syria inda gwamnatin Bashar al-Assad ke yakan masu zanga zanga dake neman gudanar da sauye sauye.

Karamin Ministan Cikin Gidan kasar ta Iraki ya tabbatar da labarin wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.