Obama da Cameron sun yi Allah waddai da rikicin Syria
Shugaban kasar Amurka Barack Obama yace luguden wutar da dakarun kasar Syria ke yi a birnin Homs abun bakin ciki ne, inda Fira Ministan kasar Birtaniya David Cameron ya zargi Gwamnati karkashin shugaba Bashar al-Assad da yunkurin hallaka mutanen kasar.
Wallafawa ranar:
Mista Cameron, wanda ke Magana a birnin Stockholm na kasar Sweden, ya nemi kawo sauyi ga gwamnatin kasar, inda yace kasashen duniya ba zasu amince da abin da ake gani a akwatunan talibijin ba, inda ake wa masu zanga-zanga dirar mikiya a birnin Homs.
A cewar shugaban, hotunan sun nuna yadda gwamnatin shugaba Al-Assad ke ci gaba da luguden wuta domin murkushe al’ummar kasar.
A jiya Alhamis ‘Yan rajin kare hakkin Bil’adama sun ce mutane 110 ne aka kashe a birnin Homs inda dakarun gwamnati ke ci gaba da kokarin murkushe masu zanga-zanga.
Kasar Jamus kuma ta yi maraba da yiyuwar sake kai ziyarar kungiyar kasashen larabawa a cikin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane 5,000 ne suka mutu tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Bashar Al Assad.
A makon jiya ne Kasar Amurka da Birtaniya suka janye jakadunsu daga kasar Syria saboda fargabar tsaro da rashin amincewa da yadda ake ci gaba da murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar al Assad.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu