Isa ga babban shafi
Pakistan-Iran-Afghanistan

Afghanistan da Iran suna gudanar da taro a Pakistan game da zaman lafiya

Shugabannin kasashen Afghanistan da Iran zasu fara gudanar da taro a Pakistan domin tattauna hanyoyin samar da zaman lafiya tsakaninsu inda zasu yi kokarin nemo hanyoyin da zasu magance matsalar kungiyar Taliban da ke addabar yankin tare da tattauna kazamar dangantakar da ke tsakanin Iran da Isra’ila.

Fira ministan kasar Pakistan Yusuf Raza Gilani yana gaisawa da Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad  kafin zamna taron da zasu gudanar a Islamabad.
Fira ministan kasar Pakistan Yusuf Raza Gilani yana gaisawa da Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad kafin zamna taron da zasu gudanar a Islamabad. REUTERS/Faisal Mahmood
Talla

Ana sa ran tattaunawar zata mayar da hankali game da samun hadin kai wajen yaki da ta’addanci da fataucin miyagun kwayoyi, da kuma huldar kasuwanci tsakanin kasashen yakin.

Shugabannin zasu tattauna kan yakin shekaru 10 da kungiyar Taliban, da yanzu dukkan masu ruwa da tsaki suka amince, sasantawa ce kawai mafitar da ta dace.

Shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari yace yana fatar taron da zasu gudanar tsakanin shi da shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad da shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai zai kasance hanyar samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

A makon nan shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai yace akwai wata tattaunawar asiri da suke yi da kungiyar Taliban amma kuma daga bisani kungiyar Taliban ta musanta haka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.