Syria
Jamia'n Tsaron Syria sun Hallaka Mutun Guda Yayin Zana'ida da Zanga Zanga
Jami’an tsaron kasar Syria sun hallaka mutun guda yayin da masu zana’idar suka gudanar da zanga zanga a Damuscus babban birnin kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Wannan daidai lokacin da jami’in kasar China ya fara ziyara tare da neman kawo karshen rikicin kasar.
Bayan ganawa da Shugaba Bashar al-Assad, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar China, Zhai Jun ya nemi dukkanin bangarorin da ke da hanu cikin rikicin kasar, su kawo karshen tashin hankalin da ke faruwa, tare gudanar da zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki wanda zai kai da zaben ‘yan majalisu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu