Isa ga babban shafi
Syria

Mai shiga tsakanin rikicin Syria Annan ya nemi hade karfi waje daya

Mai Shiga tsakani kan rikicin kasar Syria, kuma Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya bukaci duniya ta yi magana da baki guda, dan kawo karshen zub da jinin da ake ci gaba da samu a kasar ta Syria.Yayin da yake ganawa da manema labarai, Annan ya bayyana cewa yana da matukar muhimmanci, dukkan bangarori su amince da cewar, dole a samu hanya daya na sasanta wannan rikici, wanda Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Larabawa suka ba shi jagoranta. 

Kofi Annan, Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya
Kofi Annan, Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya
Talla

Gwamnatin kasar ta Syria da ake zargi da kara tsaurara matakan tsaro, ta ce tana shirya da tattaunawa da Jami'ar MDD mai kula da aiyukan agaji Vererie Amos.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.