Isa ga babban shafi
Japan

Japan ta saki kwale kwalen kasar Sin

Kasar Japan ta sako wani kwale kwalen ‘Yan kasar Sin da ta kama a yankin da ake takaddama akai tsakanin kasashen biyu.Kwale kwalen wanda ke dauke da 'Yan kasar ta Sin su bakwai ya isa gabar kasar ta Sin a yayin da mutane su ka taru suna musu marahaba.  

Wani jirgin ruwan kasar Japan
Wani jirgin ruwan kasar Japan 路透社
Talla

Rahotanni sun nuna cewa an ji mutanen da ke cikin jirgin suna wakar samun nasara inda su ke cewa ba za su saudakar da yankin ba har abada.

Kyaftin din kwale kwalen, Yeung Hong ya bayyana cewa ya ji dadi da ya dawo gida.

A cikin mutanen da ke cikin jirgin harda wasu 'Yan jarida biyu a cikin su 14 da su ka fara isa tsibrin inda bakwai daga cikinsu su ka kubuto tun farko.

Mutanen da aka sako sun bayyana cewa baza su koma wannan yanki nan kusa ba sai dai sun dauki alkawarin za su gudanar da wata zangazanga nuna bakin jinin kasar ta Japan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.