Isa ga babban shafi
Pakistan

Pakistan ta umurci kungiyar kula da yara ta Save the Children da ta fice daga kasar

Gwamnatin Pakistan ta umurci ma’aikata ‘yan kasar waje na kungiya mai kula da yara ta Save the Children, da su fice daga kasar ta Pakistan nan da sati hudu.Kungiyar wacce ke da ma’aikata ‘Yan wasu kasa ta ce har yanzu ba a gaya mata dalilin da yasa a kace su fice daga kasar ba. 

Taswirar kasar Pakistan
Taswirar kasar Pakistan
Talla

Rahotanni dai sun nuna cewa an alakanta kungiyar ne da wani likitan nan da aka yankewa hukuncin shekaru 33 bayan an same shi da hanu wajen taimakon kungiyar leken asirin kasar Amurka, CIA, wajen kashe shugaban Al Qaeda.

Kungiyar dai ta musanta cewa akwai hanunta wajen kashe shugaban na Al Qaeda.

Mai Magana da yawun bakin kungiyar, Ghulam Qadir, ya gayawa Kamfanin Dillancin labaran, AFP ya jaddada cewa, ba gaya musu dalilin da ya a aka ce su fice daga kasar ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.