Isa ga babban shafi
Pakistan

Zanga zangar kyamar fim din Amurka a Pakistan ta yi tsamari

Mummunar Zanga zanga ta barke a kasar Pakistan a yayin da Musulmai ke nuna bacin ransu game da fim din kasar Amurka da ya muzantawa addinin Islama. Mutane dauke da itatuwa sun kona wasu gidajen kallo na Sinima guda biyu a yayin da a aka raunata wani direban wani gidan talibijin, wanda wasu rahotanni ke cewa ya mutu daga baya. 

Wasu masu zanga zanga a kasar Pakistan
Wasu masu zanga zanga a kasar Pakistan Reuters/Sohail Shahzad
Talla

Zanga zangar ta biyo bayan kasashen yammacin duniya sun tsaurara matakan tsaro a ofisoshin jakadancinsu domin gudun kar a kai musu hari.

Yanzu dai akalla, an yi zanga zanga a kasashe kimanin 20 tun bayan an fitar da fim din da aka wa lakabi da ‘Innocence of Muslims’ wanda ya muzantawa addinin Islama da kuma Annabi Muhammad, wanda tsira da amincin Allah su ka tabbata a gareshi.

Kasar Faransa ma ta kulle ofisoshin jakadancinta da mnakarantu bayan a wannan satin wata mujalla ta fitar da wani zane da shi ma ya muzantawa Annabi Muhammad, wanda tsira da tsira amincin Allah su ka tabbata a gareshi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.