Isa ga babban shafi
Rasha-Birtaniya-Syria

Kasar Rasha ta bayyana baiwa ‘yan tawaye kujerar wakilcin Siriya a matsayin ba dai dai ba

Kasar Rasha ta bayyana cewar bai kamata kungiyar kasashen Larabawa ta baiwa ‘yan tawaye Kujerar wakilcin kasar Siriya ba, harma tana bayyana matakin da kungiyar kakshen Larabawan ta dauka a matsayin abinda baiyi dai dai da Dokar kasa-da-kasa ba

Ministan harkokin wajen kasar Rasha da na Faransa
Ministan harkokin wajen kasar Rasha da na Faransa
Talla

Russha tace ko a dokar kasa-da-kasa ma wannan matakin da kungiyar ta dauka ba karbabbe bane inji Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha.

A ranar Talata dai ne aka baiwa jagoran ‘yan tawayen Ahmad Moaz al-Khatib Kujerar wakilcin kasar ta Siriya a babban taron da Kungiyar kasashen Larabawa ta gudanar a Doha, matakin da ya janyo kakkausar martani daga gwamnatin kasar Siriya data bayana matakin a matsayin ganganci.

Ana dai ganin cewar kasar ta Russha na dai daga cikin abokan kawancen shugaba Bashar al-Assad ganin yadda ta yi karan tsaye ga wasu daga cikin Takunkumman da Majalisar dunkin Duniya ta kakabawa gwamnatin ta Shugaba Assad.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.