Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta soki shirin Tarayyar Turai na ceto tattalin arzikin Cyprus

Firaministab kasar Rasha, Dmitry Medvedev, ya soki shirin da kasashen Nahiyar Turai ke yin a ceto tattalin arzikin kasar Cyprus, a yayin da Minsitan kudin kasar ta Cyprus, Michalis Sarris ke shirin da hukumomin Rasha a birnin Moscow akan neman taimako.

Firaministan kasar Rasha, Dmitriv Medvedev
Firaministan kasar Rasha, Dmitriv Medvedev REUTERS/Dmitry Astakhov/RIA Novosti
Talla

“Wannan shirin da ake yi na ceto tattalin arzikin Cyprus a nawa tunanin bashi da wani amfani.” Inji Medvedev.

Kalaman Medvedev na zuwa ne a dai dai lokacin da Minista kudin Rasha, Anton Siluanov, ke shirin ganawa da Sarris a yau Alhamis bayan wata tattaunawa da aka yi a birnin Moscow.

A baya bayannan ne, ‘Yan majilusn kasar ta Cyprus suka ki amincewa da wata doka ta yi shirin cajin kudin haraji da ya kai kashi 9.9 ga masu ajiyan kudade a bankuna da kudinsi ya kai kudin Euro 20,000, a shirin da kasar ke yin a krban bashin biliyan 10 daga kungiyar Turayyar Turai.

Kasar Rasha tare da attajiranta na da fiye da kashi uku da rabin kudaden da aka ajiye a bankin kasar Cyprus, inda suke da jumallar kudi kusan biliyan 30 na kudin Euro a ajiye a bankunan kasar.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.