Isa ga babban shafi
Korea-Amurka

Ban Ki-moon ya nemi Korea ta Arewa ta sassauta barazanar Nukiliyarta

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya shaidawa Korea ta Arewa ta sassauta barazanar da ta ke yi na kai hare haren Nukiliya yana mai gargadin idan aka samu matsala lamarin ba zai haifar da abu mai kyau ba.

jiragen yakin Amurka kirar F-22  a yankin Guam
jiragen yakin Amurka kirar F-22 a yankin Guam REUTERS/U.S. Air Force/Master Sgt
Talla

Kasar Amurka, na shirin girke wani makami da ke iya cafke makamai masu linzami mai suna THAAD zuwa yankin Guam da ke tsibirin Pacific, a dai dai lokacin da sojojin kasar Korea ta Arewa ke ikirarin samun izinin kai wa Amurkar hari idan har ta kama.

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel, ya ce kasarsa na daukar wannan barazana ta Korea da matukar muhimmanci, kuma hakan na a matsayin babban hatsari a gare ta da kuma manyan kawayenta a yankin wato Korea ta Kudu da kuma Japan.

Sakataren tsaron ya ce Korea kasa ce da ta mallaki makaman nukiliya sannan kuma tana da manyan makamai masu linzami da ke da karfin gaske a halin yanzu, saboda haka take-taken kasar babbar barazana ce.

An dai kara shiga takun-saka tsakanin Amurka da Korea ne tun a cikin watan Janairun da ya gabata, bayan da Amurkar ta kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa da Korea ta kudu, sannan kuma Korea ta Kudu ta zargi Amurka da aikewa da wani jirgin yakinta domin yin shawagi a sararin samaniyarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.