Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta gargadi Korea ta Arewa akan barazanar kai harin da ta ke yi

Kasar Amurka ta yi gargadin cewa muddin kasar Korea ta Arewa ta kai mata hari to kuwa zata yabawa aya zaki. Mai Magana da yawun Ma’aikatar tsaron Amurka, a Pentagon, George Little ya ja kunnen kasar Korea ta Arewa da ta daina yiwa kasar barazana, inda ya ke cewa a shirye Amurkan take domin yin abinda ya dace. 

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama Reuters / Lamarque
Talla

Ya ce ya dace su daina duk wata barazana domin babu abinda zai haifar, domin Amurka ba zura idanu kawai za ta yi ba.

Tun ajiya Talata kasar Korea ta Arewa ta ce muddin aka nemi wuce gona da iri, a shirye take ta yi raga-raga da sansanonin sojan Amurka da na Korea ta kudu.

Barazanar da Korea ta Arewa ke yi na biyo bayan buki ne da kasar Korea ta kudu ke yi, na cika shekaru 3 da nutsar da wani jirgin ruwanta da yayi sanadiyar mutuwar sojan ruwa 46, wanda ta hakkake aikin Korea ta Arewa ce.

Korea ta Arewa dai ta musanta cewa ba ta da hanu a cikin hadarin.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.