Isa ga babban shafi
Isra'ila-Amurka-Falastine

Falesdinawa sun cancanci samun kasa mai cin gashin kanta, inji Obama

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana nuna goyon bayansa ga samun ‘yancin kasar Falesdinu a lokacin da ya ke ganawa da shugaban Falesdinawa Mahmud Abbas a birnin Ramallah. Obama yace Amurka tana fatar samun kasar Falesdinu mai cin gashin kanta.

Shugaban Amurka Barack Obama, a fadar Shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas  a Ramallah.
Shugaban Amurka Barack Obama, a fadar Shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas a Ramallah. U.S. President Barack Obama participates in a bilateral meeting
Talla

Da safiyar Alhamis ne Obama ya kai wa Faledinawa ziyara a zirin Gaza bayan ya kammala ziyara a Isra’ila.

Obama ya samu tarba ta musamman daga shugabannin Falesdinawa a ziyararsa ta farko a Gabas ta tsakiya.

Amma duk da tsauraran matakan tsaro da aka dauka a fadar shugaban Falesdinawa a Mugataa akwai daruruwan masu zanga-zanga da suka hada gangami domin nuna kyamatar ziyarar Obama a Zirin Gaza.

Ziyarar Obama a yankin Falesdinawa na zuwa ne bayan harba wasu rokoki a yankin kudancin Isra’ila daga Gaza, lamarin da shugaban na Amurka ya yi Allah waddai da shi.

A wata sanarwa, Shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas ya yi Allah Waddai da harin da aka kai a Isra’ila yana mai kira ga shugaban Hamas ya dauki matakan kawo karshen hare haren.

Tuni dai Obama ya bayyana cewa ya kawo ziyara ne Gabas ta tsakiya domin sauraren bangaren Isra’ila da Falesdinawa game da hanyoyin da za’a bi domin komawa teburin sasantawa tsakaninsu.

Faledinawa dai suna fatar Obama zai shiga tsakani domin sakin ‘Yan fursuna sama da 1,000 da Isra’ila ke tsare da su tare da ganin Isra'ila ta bude asusun tallafin da Amurka ke ba Falesdinawa na kudi kimanin Dala miliyan 700.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.