Isa ga babban shafi
Afghanistan-NATO

Harin da Sojin NATO suka kai ya hallaka akalla Yara 10 a Afghanistan

Jami'ai a kasar Afghanistan sun tabbatar da cewar wani harin da Dakarun NATO suka kai a kasar ya hallaka akalla kananan Yara 10, an dai kashe wadannan Yaran ne a yankin Shigal na Lardin Kunar, lokacin da Dakarun hadin Guiwa na NATO a kasar ke gudanar da wani samame, a cigaba da yakar 'ya'yan kungiyar al-Qaeda.

Harin da aka kai ta sama
Harin da aka kai ta sama Reuters路透社
Talla

Bayan aukuwar wannan harin da ya hallaka kananan Yara 10, wani jami'in dake cikin wannan harin da aka kai da kuma ya bukaci a boye sunan sa, yace harin ya biyo ne bayan wani harin da ya hallaka wani Sojin Amurka tare da jikkata wasu da dama.

Amma kuma Sojin da suka kai wannan harin sun bayyana cewar basuda labarin cewar akwai Mata da kananan yara a cikin wannan Gidan da suka kai samame.

Akalla an kashe Yarao 10 da Sojin sa Kai 8 da kuma Mata 6 da aka jikkata a wannan harin da aka kai inji mai magana da Yawun Lardin Kunar Wasifullah Wasifi.

Gwamnan yankin Shigal Shigal Abdul Zahir ya tabbatar da aukuwar wannan kisan, hasali ma har al'ummar garin sun kai Gawawwakin yaran a tsakiyar Gari, a yayinda aka kai Matan da aka raunata zuwa Assibiti.

Kwamandan jami'an tsaro na Shigal Sayed Rahman yace Yara 10 da Mace daya ne suka mutu, saboda daga baya an samu labarin mutuwar Mace daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.