Isa ga babban shafi
Pakistan

Kungiyar Taliban ta ce za ta kai hare-hare a ranar zaben kasar Pakistan

Kungiyar Taliban a kasar Pakistan, tayi barazanar kaddamar da hare haren kunar bakin wake ranar asabar da za’a gudanar da zaben kasa baki daya.Daya daga cikin kwamandodin kungiyar ta Taliban ne, Ehsanullah Ehsan ya sanar da shirin, wanda suka bayyana shi a matsayin matakin da ya sabawa addinin Islama.Kwamandan ya nunawa wakilin kanfanin Dillancin labaran Faransa, wasikar da shugaban kungiyar, Hakimullah Mehsud ya rubuta musu, inda ya bukaci kaddamar da hare haren kunar bakin waken.A wasikar, Mehsud ya bukaci Ehsan ya jagoranci shirya hare haren a Punjab da Sindh, yayin da shi kuma zai jagoranci na Khyber, Pakhtunkwa da Baluchistan.Akalla mutane sama da 100 aka kashe a hare haren da aka samu wajen yakin neman zaben kasar, kuma tuni kungiyar ta Taliban ta dauki alhakin kai su.Hukumomin Pakistan sun ce zasu girke jami’an tsaro 600,000 a ranar zaben.A halin da ake ciki kuma tsohon Prime Ministan kasar, Yousuf Raza Gilani ya ce wasu ‘yan bindiga, da ba a san ko su waye ba, sun sace dan shi, yayin wani yakin neman zabe. 

alamar zaben kasar Pakistan
alamar zaben kasar Pakistan
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.