Isa ga babban shafi
Afghanistan-Amurka

Amurka da Afghanistan sun samu sabani akan tsaro

Gwamnatin Afghanistan ta yi watsi da bukatar Amurka da ta bukaci a sanya hannu ga yarjejeniyar tsaro kafin karshen shekara amma shugaba Hamid Karzai ya jajirce sai an kammala zaben shugaban kasa a watan Afrilu kafin su amince da yarjejeniyar.

Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai a lokacin da ya ke jawabi a zauren Majalisar Loya jirga
Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai a lokacin da ya ke jawabi a zauren Majalisar Loya jirga REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Akwai muhawara da Majalisar Loya Jirga ta Dattawan Kabliun Afghanistan suka gudanar game da amincewa da yarjejeniyar, wanda zai tsawaita wa’adin dakarun Amurka kimanin 15,000 ci gaba da zama a Afghanistan.

A shekarar 2014 ne dakarun Kungiyar tsaro ta NATO aka shirya za su fice daga Afghanistan karkashin wata yarjejeniya da bangarorin biyu suka amince da ita. Amma sabuwar yarjejeniya za ta ba dakarun Amurka ci gaba da zama har zuwa 2024.

Shugaba Karzai yace akwai rashin yarda tsakanin shi da Amurka domin dukkaninsu babu wanda ya yarda da juna saboda sabanin da suka fuskanta a shekarun baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.