Isa ga babban shafi
China

Yau ake bukin sabuwar shekarar dawaki a China

Alummar kasar China, na bukukuwan shiga sabuwar shekara a yau, wadda suka radawa suna sabuwar shekarar Dawaki, dabbar da suke darajawa fiye da dukkan wani dabba.Miliyoyin jama a yankin Asia suka shiga ruguntsumin murnar ganin sabuwar shekarar Dawakin, da wasannin wuta da raye-raye da wake-wake da dai bukukuwa na kasaita, kamar dai yadda ake yi a bukin shiga sabuwar shekarar miladiyya.Mutane akalla miliyan 250 aka kididdige suna ta dokin tafiya wuraren da zasuyi bukin sabuwar shekarar Dawakin, domin tarago-tarago na jiragen kasa suna makare da jama’a, wasu matakiyan sun yi cikar kwari a tashoshin jiragen sama, yayinda matafiya a motoci suka yi harama.Masana dai na cewa a duniya babu irin wannan gagarumin buki, da mutane samasa miliyan 800 kowa ke dokin bukin.A aladun sinawa dai Doki na da tasiri, kuma duk wanda aka yi wa lakani da doki, to ana nufin wannan mutumin jarumi ne, kuma mai karsashi.Shugaban kasar China Xi Jinping ya fi kowa murna ayau domin yaci ado, kamar yadda aka nunashi a jawabin musamman day a yi ‘yan kasar da fatan alheri, bayan yayi ta shan hannu da mutane, albarkacin wannan rana ta Dawaki. 

Wasu Chinisawa suna bukin shiga shekarar dawaki
Wasu Chinisawa suna bukin shiga shekarar dawaki REUTERS/Kim Kyung-Hoon
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.