Syria : Brahimi ya yi murabus
Bayan shafe tsawon lokaci yana kokarin kawo karshen yakin basasan kasar Syria ba tare da nasara ba, mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Hadin kan kasashen Larabawa Lakhdar Brahimi ya bayar da sanarwar yin murabus.
Wallafawa ranar:
Brahimi zai ajiye aikin shiga tsakanin rikicin Syria daga ranar 31 ga wannan watan na Mayu
Brahimi Dan Asalin kasar Algeria, mai shekaru 80 a duniya, ya sami nasarar kawo bangaroron gwamnatin Bashar al-Assad, da ‘yan tawayen Syria su shiga tattaunawar zaman lafiyan da aka shirya a birnin Genevan kasar Switzerland har sau 2, a bana.
Sai dai wannan karon, kokarin na Brahimi ya gagara kawo karshen yakin basasar Syria, da ya lakume rayukan fiye da mutane dubu 150, wasu miliyoyi kuma suka rasa gidajen su cikin shekaru uku.
Kokarin sasanta rikicin na Syria ya sake samun koma baya, sakamakon takun saka tsakanin Amurka da Rasha, kasashe biyu da ke tallafawa Brahimi, da kuma yanzu ke cacar baki kan makomar kasar Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu