Isa ga babban shafi
Iran-Iraq

Iran ta ce Amurka ta rasa al-Qibla a kan rikicin kasar Iraqi

Kasar Iran ta yi kira da a kafa sabuwar Gwamnati a Iraqi saboda abinda ta kira kasawar Gwamnatin Nuri al-Maliki na magance tashin hankali a kasar. Iran hakama ta sammaci Amurka da zama maras al-Qibla kan rikicin na kasar Iraqi da ko a yau an bada labarin kisan akalla jami'an tsaro 34

independent.co.uk
Talla

Babban malamin addinin musulunci a kasar ta Iran Ayatoullah Ali al-Sistani ne, ya bayyana bukatar kafa kwakkwarar Gwamnati da za ta kasance karbabbiya ga daukacin al’ummar kasar domin kaucewa dambarwar da aka sama a baya.

Shima dai mataimakin Ministan harkokin waje na kasar ta Iran Hossein Amir Abdullah, ya maidawa shugaba Barack Obama na Amurka martani kan kalaman da ya yi cewar suna kokarin sake aika Dakaru 100 a kasar ta Iran.

Yace Obama da Gwamnatinsa sun rasa madafa kan matsalar Iraqi duk da shekarun da suka kwashe suna zaman dirshan a cikin kasar.

Yanzu haka dai Firaiministan Iraqi Nuri al-maliki da ke neman sake komawa karagar mulkin kasar bayan zaben da aka yi a ran 30 ga Watan Afrilu na, huskantar babban kalubale a cikin kasar da kuma waje.

Ko da sanyin Safiyar yau ma an bada labarin wata arangama da aka yi da masu tada Kayar baya na Sunni a cikin Samalainin Dare, inda aka ce akalla mutane 34 ne suka kwanta Dama kai tsaye.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.