Isa ga babban shafi
Malaysia

An cika shekara guda da bacewar jirgin saman kasar Malaysia

Jiya Lahadi al’ummar kasar Malaysia suka gudanar da adduo’i na musanman don cikar Shekara guda da bacewa jirgin saman kasar mai lamba MH 370, da yayi batan dabo. Wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da gudanar da bincike don gano jirgin, da ya tashi daga birnin Kuala Lampur ya nufi birnin Beiging na kasar China dauke da fasinjoji 239.Jirgin dai ya tashi ne daga filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Kuala Lampur, kuma kawo yanzu babu wani takaimaimen bayani game da jirgin da ake kyauta zaton ya fadi ne acikin tekun India. Dangin fasinjojin jirgin sun bayyana matukar damuwarsu, musanman ma yadda gwamnatin kasar ta Malaysia ta kasa basu bayani mai gamsarwa game da batan jirin. Sai dai kuma a yayin jawabinsa Fraiministan kasar ta Malaysia Najib Razak, ya bayyana damurwasa, inda yace al’ummar kasar zasu cigaba da addu’a da fatan masu bincike zasu gano jirgin a nan gaba, sannan ya kara da cewa bashi da wata kalma da zai bayyana halin kunci da gwamnatinsa da iyalan fasinjojin da hadarin ya rutsa da su ke ciki, tun bayan batan jirgin.Masu bincike dai sun gagara gano koda tarkacen jirgin ne da a wani lokaci suka ce ya fada tekun India ne. Yanzu dai Fraiminista Najib Razak yace al’ummar kasar ta Malaysia zasu cigaba da addua tare da fatar ko bajima ko ba dade za’a gano ainihin abinda ya faru da jirgin mai lamba MH 370. 

Wasu dangin mutanen dake cikin girgin saman kasar Malaysia mai lamba MH 370
Wasu dangin mutanen dake cikin girgin saman kasar Malaysia mai lamba MH 370
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.