Isa ga babban shafi
Masar

Kungiyar Larabawa ta nemi hadin kai don yakar IS

Kugiyar Hadin kan kasashen Larabawa ta nemi a gagauta samar da wata runduna, da za ta yi yaki da kungigiyoyi masu tsatstsauran ra’ayi a yankin.

Nabil al-Arabi, Sakataren kungiyar Larabawa
Nabil al-Arabi, Sakataren kungiyar Larabawa REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Shugaban kungiyar Nabil al-Arabi ne ya yi wannan kiran, inda ya bayyana muhimmancin hadin-kai ta fannin tsaro da musayar bayanai tsakanin kasashen Larabawa.

Nabil al-Arabi dake magana yau Litinin, yayin taron kungiyar da ake yi a birnin Alkahiran kasar Masar, yace rundunar zata taimaka wajen yaki da ayyukan ta’addanci da ma kungiyoyin ‘yan ta’adda.

A makon da ya gabata, mataimakin shugaban kungiyar ta hadin kan kasashen larabawa Ahmed Ben Helli ya shaida wa ‘yan jarida cewa ana sa rai shugabannin yankin su mayar da hankali wajen samar da irin wannan rundunar, a yayin taron su na ranakun 28 da 29 ga wannan watan.

Shima shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya nemi a samar da irn wannan rundunar a yankin, don fuskantar barazanar da ake samu da kungiyar ISIS dake rike da yankuna da dama a kasashen Iraqi da Syria, da kuma ta bulla a kasar Libya.

Kasashen larabawa da dama suna bayar da talafi a hare haren sama da Amurka ke jagoranta kan mayakan na ISIS a Syria, yayin da Masar ta kaddamar da nata harin kan ‘yan kungiyar da suka sami shiga Libya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.