Isa ga babban shafi
Iran-Isra'ila

Ba dole ne Iran ta amince da Isra’ila a matsayin kasa ba, inji Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama, ya ce neman Iran ta amince da Isra’ila a matsayin kasa, ba ya daga cikin batutuwan da ke kunshe a cikin yarjejeniyar Nukiliya da aka kulla da kasar cikin makon da ya gabata

U.S. President Barack Obama speaks about the framework agreement on Iran's nuclear program announced by negotiators in Switzerland during a statement in the Rose Garden of the White House in Washington April 2, 2015
U.S. President Barack Obama speaks about the framework agreement on Iran's nuclear program announced by negotiators in Switzerland during a statement in the Rose Garden of the White House in Washington April 2, 2015 REUTERS/Mike Theiler
Talla

A hukumance dai Iran ba ta amince da wanzuwar wata kasa mai suna Israel ba, yayin da take kallon kasar a matsayin wani sansani na ‘yan mamaya.

Wannan matsayin na Iran kan wanzuwar kasra Isra’ila dai, na daga cikin abubuwan da isra’ila ke kallo a matsayin babbar barazana a wurinta, musamman idan iran ta samu karfin fada a ji a yankin kasashen Larabawa.

Isra’ila dai ta tsargu ta ga an kammala tattaunawar da ake tsakanin Iran da manyan kassahen Duniya, da kuma fatar Iran ba za ta samu matsayin da take bukata ba.

Ko a bayan nan ma wannan batu na kasar Isra’ila da Iran ya janyo tada jijiyoyin wuya tsakanin ita Isra’ila da abokiyar kawancenta Amurka da Isra’ila ke kallo a matsayin mai y iwa batun rikon Sakainiyar Kashi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.