Isa ga babban shafi
Malaysia-Ukraine

An fara tsintso baraguzai jirgin Malaysia

Masu bincike na Kasar Netherland sun tsinto wasu sassan jikin mutane da kuma wasu buraguzai a yankin da Jirgin Kasar Malaysia ya yi hatsari a Kasar Ukraine.

Wasu daga cikin kayayyaki Fasinjojin MH17 da aka tsinto
Wasu daga cikin kayayyaki Fasinjojin MH17 da aka tsinto © Sébastien Gobert
Talla

Jirgin samfurin MH17 wanda yayi hatsari a bara, a yankin gabashin Ukraine, wanda ake zargin ‘yan tawayen Kasar da ke tada kayar baya suka harbor, akalla mutane 298 ne suka rasa rayukansu.

Gwamantim Kasar Netherland ta bayyana cewa, masu binciken sun gano wasu sassan jikin mutane a cikin ‘yan kwanaki kadan da fara gudanar da binciken, yayin da kuma suka tattara kayayyakin Fasinjojin jirgin da suka hada da kayan adon mata, takardun shedar tafiye-tafiye da kuma hotunan Fasinjojin.

Yanzu haka dai, kayayyakin da aka gano za’a kai su birnin keiv da ke Ukraine, kafin a yi gaba da su zuwa kasar Netherland.

A makon daya gabata ne dai aka fara gudanar da sabon binciken a Petropavlivka da ke da tazarar kilomita 10 daga yankin da aka samu akasarin buraguzan jirgin.

Gwamantin Kasasr Ukraine da kasashen yammaci sun ta bayyana cewa, ‘yan arewacin Ukraine ne suka kakkabo jirgin, inda suka yi amfani da makami mai linzami da ake zargin Rasha ta ba su, Zargin da Rasha ta musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.