Mummunar Girgizan kasa ta abka wa Nepal
Mutane sama da 4,000 aka ruwaito sun mutu sakamakon wata mummunar girgizan kasa da ta abkawa sassan yankunan Nepal tun a ranar Assabar. Hukumomin kasar sun ce adadin wadanda suka mutu na iya zarce haka anan gaba saboda akwai daruruwan mutane da gini ya rubta da su sakamakon girgizan kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Girgizan kasar mai girman maki 7.8 ta shafi yankunan Kathmandu babban birnin Nepal da wasu yankuna zuwa tsaunin Everest kusa da yankin India da Bangladesh.
Kungiyoyin agaji daga kasashen duniya da dama na ci gaba da kai dauki zuwa kasar Nepal bayan daruruwan mutane sun mutu.
Rahotanni sun ce girgizan kasar ta lalata hanyoyin sadarwa da kaste wutar lantarki tare da lalata hanyoyin ababen hawa lamarin da kuma ke kawo tarnaki ga aikin jami’an agaji.
Tuni dai Amurka da Faransa da kungiyar Tarayyar Turai suka aika da Jami’an agaji da kudaden tallafi zuwa Nepal.
Yanzu haka gwamnatin Nepal ta kafa dokar ta-baci a yankunan da girgizan kasar ta shafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu