EU ta ce akwai 'yan kasashenta da suka bata bayan girgizar kasar Nepal
Kungiyar Kasashen Turai ta ce har yanzu akwai wasu ‘yan kasashenta dubu 1, da ba su ji duriyar su ba tun bayan aukuwar mummunar Girgizar kasa a Nepal ya kashe dubban mutane
Wallafawa ranar:
Jakadan Kungiyar Kasahen Turai a Nepal, Rensje Teerink ya ce, akwai yan kasashensu da dama dake zuwa tsaunin Everest kusa da inda Girgizar kasar mai girman maki 7.8 ta shafa a Kathmandu babban birnin kasar
Rensje ya ce, har yanzu basu da labari dangane da halin da ‘yan kasashensu a yankin ke ciki, sai dai ana zatan watakila wasun su na yankin da wayar sadarwa bata kai wa.
Rahotannin na cewa, Mutane da dama mummunar girgizar kasar ta shafa na cewa, ba su samu komai na taimako ba, kusan mako guda bayan aukuwar bala'in.
Gwamnatin Nepal na cigaba da yin kira ga gwamnatocin kasashen waje da su kara aikawa da jirage masu saukar ungulu domin kai kayan agaji zuwa wurare masu nisa dake yankunan tsaunuka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu