Akwai yiwuwar barkewar cututtuka a Nepal
Bayan afkuwar bala’in girgizan Kasa a Nepal, kwararru sun bayyana cewa, akwai yiwuwar barkewar cututtuka, sakamkon ruwan masai daya karade wurare da kuma yadda gawarwaki da ke ci gaba da doyi, yayin da dubban mutane ke kwanciya a sararin Allah.
Wallafawa ranar:
lamarin dai ya tada hankulan kwararru, wanda ke dari-darin yiwuwar barkewar cututtuka tsakanin al-ummar kasar
An taba samu irin wannan lamarin a kasar Haiti a lokacin data gamu da bala’in girgizan kasa a shekara ta 2010, inda cutar kwalara ta yadu tsakanin al-umma saboda gurbacewar ruwan sha bayan aukuwar girgizan kasar.
Patrick Fuller, babban jami’i ne a hukumar bada agajin gaggauwa ta Red Cross, ya shaidawa kamfanin dillacin labaran faransa cewa, akwai yiwuwar samun cututtuka kamar amai da gudawa tsakani al-umma dake shan gurbatattacen ruwa a yanzu
Kawo yanzu dai, dubban jama’a ne suka shafe tsawon kwanaki biyar a sararin Allah a Kathmandu babban birnin kasar Nepal, yayin da kuma suka rasa tsaftataccen ruwan sha kuma suke bahaya a filin da su ke.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu