Isa ga babban shafi
Nepal

Mutane Miliyan 8 girgizan kasa ta shafa a Nepal

Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane miliyan 8 mummunar girgizan kasa ta shafa a kasar Nepal, kuma ta bukaci kai agajin gaggawa a kasar domin dubban mutane ke bukatar tallafin Abinci, yayin da adadin wadanda suka mutu ya zarce 4,000.

Mutanen kasar Nepal da bala'in Girgizan kasa ta shafa
Mutanen kasar Nepal da bala'in Girgizan kasa ta shafa REUTERS/IFRC/Palani Mohan
Talla

Tun a ranar Assabar ne girgizan kasar mai karfin maki 7.8 ta abkawa kasar Nepal inda ta rusa gidaje a Kathmandu tare da lalata hanyoyin ababen wa da katse hanyoyin sadarwa.

Yanzu haka kayan agaji sun fara isa kasar daga kasahsen duniya yayin da dubban mutane ke ci gaba da kwana a sararin Allah saboda rashin matsuguni.

Muhimman bukatun ‘yan kasar sun hada da ruwan sha da abin da zasu ci da magani da kuma jakar ledar sanya gawarwaki.

Mai Magana da yawun ma’aikatar cikin gidan kasar Laxmi Prasad Dhakal ya ce adadin mutanen da aka tabbatar da mutuwar su ya kai 4,310, yayin da ake cigaba da neman wasu da gine gine ya rubta da su.

Jami’in ya kuma ce mutane 7,953 suka samu raunuka

Kasar Amurka ta ce zata aikawa Nepal agajin Dala miliyan 10 a matsayin agaji don tallafawa mutanen da girgizar kasar ya ritsa da su.

Ma’aikatar tsaron kasar ta kuma umurci zaratan sojojinta 24 da ake kira Green Beret, wadanda ke kasar da su taimakawa hukumar agajin gaggawa wajen ceto wadanda hatsarin ya ritsa da su.

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Kanar Steven Warren yace sojojinsu da dama suke wani atisaye a tsaunin Mount Everest tuni suka shiga aikin ceto a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.