Isa ga babban shafi
Nepal

Mutanen da suka mutu a Nepal sun zarce 5,000

Ana ci gaba da kai kayan agaji ga dubban mutanen da bala’in girgizar kasar Nepal ya shafa a kauyuka da birnin Kathmandu, yayin da adadin mutanen da aka tabbatar da mutuwarsu ya zarce 5,000 yanzu haka.

Girgizan kasa a Nepal ta rusa gidaje da katse lantarki tare da raunata mutane da dama
Girgizan kasa a Nepal ta rusa gidaje da katse lantarki tare da raunata mutane da dama Claire Wissing/ RFI
Talla

Firaministan kasar Sushil Koirala ya ce saboda aikin kai dauki ga mutanen da ke kauyuka na da wahalar gaske saboda rashin isassun jiragen sama masu saukar ungulu.

Koirala da ya yi jawabi ga al’ummar kasar ya bayyana zaman makoki na kwanaki uku da kuma sake kira ga kasashen duniya da su yi wa Allah su taimaka mu su.

Rahotanni sun ce mutanen da suka mutu sakamakon girgizan kasar a kasashen China da India da ke makawabtaka da Nepal sun zarce 100.

Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane miliyan 8 mummunar girgizan kasa ta shafa a kasar Nepal, kuma ta bukaci kai agajin gaggawa a kasar domin dubban mutane ke bukatar tallafin Abinci, yayin da adadin wadanda suka mutu ya zarce 4,000.

Tun a ranar Assabar ne girgizan kasar mai karfin maki 7.8 ta abkawa kasar Nepal inda ta rusa gidaje a Kathmandu tare da lalata hanyoyin ababen wa da katse hanyoyin sadarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.