Isa ga babban shafi
Syria-ISIL

Kurdawa na samun nasara akan ISIL a Syria

Mayakan kurdawan kasar Syria sun sake samun nasarar fatattakar mayakan Jihadin kungiyar ISIL, daga wani gari mai matukar muhimmanci a yankin kan iyakar kasar da kasar Turkiya.

kurdawa da ke  farma ISIL a Syria
kurdawa da ke farma ISIL a Syria Reuters/路透社
Talla

Al’amarin da ya sa a cikin mako guda, garuruwa biyu masu matukar muhimmanci suka kubuce daga hannunsu.

Wannan dai wani sabon koma baya ne ga mayakan ISIL a yankin arewacin kasar Syria, mako guda bayan da garin Tal Abyad, da ke kan iyakar kasar da Turkiya ya kubuce daga hannunsu.

Mayakan na ISIL dai sun sha barin wutar da dakarun kurdawa suka yi masu, al amarin da ya tilasta musu tserewa daga garin na 'Ain Issa, mai tazarar kilo mita 50 da garin Raqqa, tingar Mayakan Islamar a cikin kasar Syria.

Za a iya cewa dai wannan wani ci gaba ne, mai matukar muhimmanci ga dakarun na kurdawan kasar ta Syria a kan mayakan Jihadin, a cewar, Issa Khaled, wakilin kungiyar neman yancin kurdawa ta PYD a kasar Faransa.

Khaled ya ce Wannan na nuna cewa duk lokacin da 'yan ta’adda suka tsinci kansu a gaban gungun dakarun da aka horar da kyau, kuma ke dauke da wadatattun makamai ba za su iya yin wani tasiri ba.

Khaled dai na gani cewar, wannan zai iya haifar da sanyin guiwa ga 'yan ta’addan,nan gaba kafin su kai wani sabon hari za su tsaya su dora wa kansu kalaman tambaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.