Isa ga babban shafi
Serbia

Firiya Minsiatan Aleksandar Vucic ya sha ruwan duwatsu

Wani harin ruwan duwatsu da ya auku a dai-dai lokaci da ake gudanar da jimamin tunawa da kisan da akayi wa musulmi Serbia dubu 8 a Bosnia, ya haifar da hargitse, tare da tilastawa Friya Minista kasar Aleksandar Vucic tserewa domin neman mafaka.

Firiya Ministan Serbia Aleksandar Vucic da takwaransa na Albania
Firiya Ministan Serbia Aleksandar Vucic da takwaransa na Albania REUTERS/Marko Djurica
Talla

Shekaru 20 kenan da aukuwar kisan gilar da akayiwa Muslmi Serbiyawa, kuma a yau asabar dubun dubatan mutane ne suka taru domin gudanr da addu’o ‘i ga mamatan.

Sai dai wasu daga cikin cuncurundo mutane da suka fusata a lokacin taron sun yi amfani da duwatsu wajan jifar, al’amarin da ya kai ga fasa gilashin Firiya Ministan.

Duk da haka dai Aleksandar Vucic ya ce ba zai daina kokarin da yake ba wajen kawo karshan duk wani rikici da ke akwai tsakanin Serbia da Bosnia domin kula kyakyawa danganta tare da yafewa juna.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.