An kama mutane 7 saboda kisan gilla a Serbia
Jami’an tsaron Kasar Serbia sun tsare mutane 7 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yiwa mutane da dama a shekarar 1995, kuma shine karon farko da hukumomin kasar suka gudanar da wannan irin kamen
Wallafawa ranar:
Mutanen da ake zargin da kuma ba’a ambaci sunayensu, na daga cikin Mambobin wata Kungiya a Bosnia.
Akalla Mutane dubu 8 ne da kananan yara, aka kashe, yayinda aka jibge gawawwakinsu a wani rami mai fadin gaske a lokacin kisan gillar na Serbiyawan Bosniya da aka bayyana a matsayin mafi kamari da aka gani a Nahiyar Turai tun bayan yakin duniya.
Masu gabatar da karan, na cigaba da bukatar gano karin wasu mutane da aka ce an kashe a makwabtan kasashe a lokacin da aka gudanar da kisan gillar.
Wadanda aka Kaman kuma, Mambobin wata kungiyar Serbiyawan Bosniya na Joharina ne, da aka ce suna da hannu a kisan gillar na ranar 13 ga watan yulin shekara ta 1995.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu