Isa ga babban shafi

An yi bikin kunna wutar gasar Olympics da za ta gudana a birnin Paris

Yau Talata aka kunna wutar gasar Olympics da birnin Paris ke shirin karɓa nan da ‘yan watanni.

Hannun jarumar fina-finan kasar Girka Mary Mina daga ɓangaren dama yayin kunna wutar gasar Olympics a garin Olympia na ƙasar Girka mai tsohon tarihi.
Hannun jarumar fina-finan kasar Girka Mary Mina daga ɓangaren dama yayin kunna wutar gasar Olympics a garin Olympia na ƙasar Girka mai tsohon tarihi. AP - Thanassis Stavrakis
Talla

Bikin na gargajiya ya gudana ne a garin Olympia mai tsohon tarihi da ke Girka, matakin da ke nuna kai wa gaɓar ƙarshe na shirye-shiryen da aka shafe shekaru bakwai ana yi kan gasar da za a fara a ranar 26 ga watan Yuli.

Jarumar fina-finan kasar Girka Mary Mina, da aka zaɓa a matsayin jagorar bikin gargajiyar ce ta kunna wutar Olympics ɗin, gasar da karo na uku kenan da Faransa za ta karɓi baƙuncinta a birnin Paris bayan hakan da ta yi a shekarun 1900, da kuma 1924.

Bikin gargajiya na kunna wutar gasar wasannin Olympics da birnin Paris zai fara karɓar baƙunci a ranar 26 ga watan Yuli.
Bikin gargajiya na kunna wutar gasar wasannin Olympics da birnin Paris zai fara karɓar baƙunci a ranar 26 ga watan Yuli. AP - Thanassis Stavrakis

Yayin jawabin da ya gabatar shugaban kwamitin shirya gasar Olympics na duniya Thomas Bach, ya ce ko shakkah babu mutane sun kosa a fara wasannin motsa jikin domin ɗebe musu kewa daga tashe-tashen hankulan da suke ƙaruwa da suka kunshi, ta’addanci da kuma munanan labarai.

A makon da ya gabata shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce za a buƙaci Rasha ta tsagaita buɗe wuta a Ukraine yayin gudanar gasar ta Olympics, kamar yadda aka saba mutunta wasannin a lokutan baya, sai dai Rasha ta ki amincewa da tsarin bisa zargin cewa Ukraine za ta iya amfani da damar wajen sake kintsawa yakin da suke gwabzawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.