Isa ga babban shafi

Fafaroma Francis zai share kwanaki 12 a Asiya a watan Satumba

A watan Satumbar shekarar bana ne Fafaroma Francis zai kaddamar da ziyarar aiki zuwa kasashen  Indonesia, Papua New Guinea, Gabashin Timor da Singapore duk da fama da rashin lafiya da shugaban darikar katolikan ta duniya mai shekaru 87 ke fama da ita.

Fafaroma Francis saman keken guragu
Fafaroma Francis saman keken guragu via REUTERS - POOL
Talla

 

Wannan ziyara na daya daga cikin balaguro mai nisan kilometa  30,000  da Fafaroma zai yi tun vayan hawansa kujerar shugabancin fadar Vatican a shekara ta 2013.

A wannan tafiya Fafaroma zai ziyarci Jakarta daga 3 zuwa 6 ga Satumba, Port Moresby da Vanimo daga 6 zuwa 9 ga Satumba, Dili daga 9 zuwa 11 ga Satumba da Singapore daga 11 zuwa 13 ga Satumba,rabon da Fafaroma ya gudanar da wata tafiya zuwa kasar waje tun a watan satumban shekarar da ta shude sabili da fama da rashin lafiya,wasu lokutan an lura cewa ya na baiwa mataimakansa damar karanta da yawa daga cikin jawabansa.

Fafaroma Francis a fadar Vatican
Fafaroma Francis a fadar Vatican AP - Alessandra Tarantino

Fafaroma Francis da ke famada cutar sankarau,rashin lafiyar ta kai shi ga amfani da keken guragu, bayan fama da ciwon gwiwa.

Idan aka yi tuni a shekarar 2020 ne Fafaroma Francis ya dace ya ziyarci wasu kasashen da suka hada da Papua New Guinea, Gabashin Timor da Indonesia, aka kuma soke wanan tafiya saboda cutar amai da gudawa.

Fafaroma Francis gaban mabiya darikar Katolikan
Fafaroma Francis gaban mabiya darikar Katolikan AFP - HANDOUT

Tun bayan zama Fafaroma,shekaru 11 da suka gabata, Fafaroma Francis ya yi balaguro 44 zuwa kasashen waje, na baya-bayan nan zuwa Marseille na kasar Faransa a watan Satumba.

Ya kuma bayyana shirin zuwa Belgium a wannan shekara, yayin da ya bayyana yiwuwar ziyarar gida a Argentina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.