Isa ga babban shafi

Limaman Katolika sun ci zarafin yara dubu 5 a Portugal

Hukumomin kasar Portugal sun fitar da wani rahoton bincike da ke nuna cewa kusan yara 5,000 ne limaman cocin Katolika suka ci zarafinsu tun daga shekarar 1950 zuwa yanzu.

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis.
Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis. AP - Alessandra Tarantino
Talla

Wani kwamiti na musamman da ke bincike kan wannan ta’asar ya tabbatar da cewa sun saurari korafe-korafe daga daruruwan yaran da aka ci zarafi a Portugal.

Rahotanni kan yadda aka ci zarafin dubban yara a Cocin Katolika dai na ci gaba da yawo a duniya, abin da ya sa shugaban Mabiya Darikar Katolika na Duniya Fafaroma Francis ke fuskantar matsin lamba game da kawo karshen matsalar.

Binciken, wanda Cocin a kasar mai kishin Katolika ya ba da umarni, ya wallafa sakamakon bincikensa bayan jin ta bakin mutane fiye da 500 da abin ya shafa a bara.

A cewar kwamitin, wannan shaidar ce, ta ba shi damar fitar da korafe-korafe na wadanda abin ya shafa, na akalla 4,815, ”in ji shugaban kwamitin Pedro Strecht a wani taron manema labarai a Lisbon wanda ya sami halartar manyan jami’an Cocin.

Strecht, wanda ya kasance likitan kula da lafiyar kwakwalwar yara, ya ce zai yi wahala yanzu Portugal ta iya kawo karshen matsalar lalata kananan yara.

Yayin da yake fuskantar kalubale kan dimbin laifukan cin zarafin na limaman coci da suka fito fili a duniya da kuma zargin yin rufa-rufa, Fafaroma Francis ya yi alkawari a shekarar 2019 don kawar da matsalar lalata kananan yara a Cocin Katolika.

An kaddamar da bincike a kasashe da dama baya ga Portugal, da suka hada da Australia, Faransa, Jamus, Ireland da Netherlands, duka dai kan yadda limaman coci ke lalata rayuwar kananan yara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.