Isa ga babban shafi

Vatican ta amince limamanta su sanya wa masu mu'ammalar jinsi guda albarka

A Litinin Fadar Vatican ta sanar da cewa Paparoma Francis ya amince da wani gagarumin hukunci na cewa limaman darikar Roman Katolika na iya sanya albarka a auren masu jinsi daya muddin hakan ba zai kasance cikin jerin al’adun cocin na yau da kullum ba. 

Fafaroma Francis.
Fafaroma Francis. REUTERS - GUGLIELMO MANGIAPANE
Talla

Wata takarda daga ofishin bishara na fadar Vatican, da ta yi watsi da matakin fadar na shekarar 2021, ta ce hakan ba ya nufin halasta al’amuran da ba su dace ba, amma alama ce da ke nuna cewa Allah na maraba da kowa.

Sanarwar fadar Vatican ta ce wannan mataki bai sauya matsayin majami’ar Katolika a game da aure ko mu’ammalar jinsi daya ba, tana mai cewa aure  ya halasta ne tsakanin miji da mace da zummar hayayyafa.

A shekarar 2021, fadar Vatican ta ce ikilisiya ba ta da damar sanya albarka a auren masu jinsi guda, tana mai cewa ba yadda za a yi Allah ya yi wa zunubi albarka.

A sanarwarta ta wannan Litinin, Vatican ta ce ba a yarda a yi amfani da tufafi ko wata alama, ko kuma amfani da addu’o’in da ake yi wajen daurin auren miji da mace a lokacin auren masu jinsi guda ba.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.