Limamin coci a Vatican zai yi zaman kaso na sama da shekaru 5 saboda rashawa
Wata kotu a Vatican ta yanke wanni babban limamin coci dan kasar Italiya hukuncin daurin shekaru 5 da rabi a gidan kaso sakamakon samun sa da hannu a laifin almundahana da kudade.
Wallafawa ranar:
Angelo Becciu, mai shekaru 75, wanda tsohon mai bai wa Fafaroma Francis shawara ne, ya taba zama daga cikin wadanda ake ganin za su iya rike mukamin Fafaroma a Vatican, kuma shine limamin Katolika mafi girma da ya taba gurfana a kotun Vatican saboda aikata laifin da ya shafi rashawa.
Becciu da wasu mutane tara sun gurfana a gaban kotun ne don kare kansu a kan badakalar sayar da kadarorin Vatican a Landan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu