Leonel Messi ya dawo taka leda bayan dawowarsa daga jinya
Bayan dawowar Lionel Messi daga jinya, ya yi nasarar jefawa kungiyarsa ta Inter Miami kwallo a ragar Colorado Rapids a wani wasa da suka kara.
Wallafawa ranar:
Zura kwallon da Messi ya yi sanya kungiyar ta yi canjaras da abokiyar karawarta ta Colorado Rapids yayin da suka tashi da ci 2-2.
Dan wasan dan kasar Argentina dai bai samu damar buga wasanni hudu ba a sakamakon raunin da ya samu, kuma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sai kungiyar tasa ta jefa 1-0 bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida da Rafael Navarro ya jefa.
Mesin ne dai ya taimaka wajen kara zura kwallo a ragar Colorado Rapids a yayin da ya ba wa Leonardo Afonso da suke kungiya daya.
Kungiyar Miami dai ba ta kai ga samun nasara ba a wasan yayin da dan wasan kungiyar Colorado Rapids ya antayawa Inter Miami kwallo a raga wadda ta sanya aka tashi canjaras wato ci 2-2.
Miami ta gagara ci gaba da jan ragamar wasan ne dai bayan da Cole Bassett ya ramawa Rapids a minti na 88 da fara wasan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu