Isa ga babban shafi

Yaƙin Gaza: An ci gaba da kama masu zanga-zanga a harabar jami'o'in Amurka

‘Yan sanda sun tarwatsa gungun masu zanga-zanga a jami’ar Texas ta ƙasar Amurka, inda suka kama gwamman mutane, a yayin zanga-zangar nuna adawa da yaƙin da Isra’ila ke yi da Hamas a zirin Gaza, zanga-zangar da ta mamaye jami’o’i da dama a ƙasar.

Wani dallibi da 'yan sanda suka kama ayayin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a jami'an Texas ta Amurka.
Wani dallibi da 'yan sanda suka kama ayayin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a jami'an Texas ta Amurka. Getty Images via AFP - BRANDON BELL
Talla

Jami’an ‘yan sanda sun kuma tsare mutane da dama a jami’ar Fordham ta jihar New York,kana suka cire dukkannin shingayen da aka kafa a harabar jami’ar, kamar yadda mahukunta suka bayyana, kana aka jibge jami’ai a jami’ar Colombia don ko ta kwana, bayan kame da aka yi na dimbim ɗalibai a ranar Laraba.

A cibiyar fasaha ta Massachusetts, masu zanga-zangar sun tona wani rami, wanda ya datse wani layi a tsakiyar harabar makarantar a Cambridge, a yayin zanga-zangar da ta yi ƙamari a ranar Laraba.

Bugu da ƙari, gwamman motocin ‘yan sanda ne suka yi sintiri a jami’ar California a matsayin martani ga tarzomar da ta tashi a cikin dare, lokacin da masu adawa da zanga-zangar suka suka kai wa masu goyon bayan Falasdinawa hari.

Yaƙin Gaza ya ɓarke ne bayan da Hamas ta shammaci Isra’ila, inda ta kai mata wani hari da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane dubu 1 da dari 1 a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023.

Maharan sun kuma yi garkuwa da kimanin mutane 250.

Ya zuwa yanzu hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza ya kashe sama da Falasdinawa dubu 34, kamar yadda ma’aikatar lafiyar Gaza ta sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.