Isa ga babban shafi

Fafaroma ya bukaci 'yan kasar Hungary da su bude kofa ga bakin haure

Fafaroma Francis a yau lahadi ya yi kira ga ‘yan kasar Hungary da su “bude kofa” ga bakin haure, a daidai lokacin da ya kammala ziyarar kwanaki uku a kasar dake tsakiyar Turai karkashin jagorancin firaministan mai tsananin kyamar bakin haure.

Fafaroma Francis a kasar Hungary
Fafaroma Francis a kasar Hungary © VATICAN MEDIA / via REUTERS
Talla

Fafaroma da a duk lokacin da ya kai ziyara Budapest na kasar ta Hungary ya na jaddada matsayin maraba ga wadanda ke gujewa rikici ko talauci da aka sani da bakin haure.

Kalaman sun bambanta da na Firaministan Hungary Viktor Orban.

Fafaroma Francis tareda Victor Orban
Fafaroma Francis tareda Victor Orban © VATICAN MEDIA / REUTERS

Orban ya yi maraba da 'yan gudun hijirar Ukraine tareda furta kalaman  kare manufofin Turai tun bayan hawan sa mulki a 2010.

Akala mutane 50,000 ciki har da Firaminista Orban, sun saurari Fafaroma Wanda ya jagoranci wani taron bude baki a dandalin Budapest dake tsakiyar kasar karkashin tsauraran matakan tsaro.

A yayin taron, Fafaroma dan kasar Argentina mai shekaru 86 ya bukaci kowa da kowa, gami da masu alhakin siyasa da zamantakewa, da su kara bude ido.

Fafaroma ya na mai cewa don Allah, ku bari mu buɗe waɗannan kofofin!

Fafaroma  Francis, tareda Shugabar kasar Hungary  Katalin Novak da Firaminista  Victor Orban
Fafaroma Francis, tareda Shugabar kasar Hungary Katalin Novak da Firaminista Victor Orban REUTERS - MARTON MONUS

 Ya kara da cewa "abin bakin ciki ne da raɗaɗi... ganin kofofin da aka rufe".

A karshen taron Fafaroman ya yi addu’a ga ‘yan Ukraine  da ke fama da rikici da kuma al’ummar Rasha.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.