Isa ga babban shafi
Rasha - Ukraine

Hungary ta yi tayin karbar bakuncin taron sulhu tsakanin Rasha da Ukraine

Gwamnatin kasar Hungary ta gabatar da tayin karbar bakuncin tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine, bayan shiga rana ta biyu a yakin da Rasha ta kaddamar kan makwabciyarta.

MInistan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov tare da takwaransa na Rasha Peter Szijjarto.
MInistan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov tare da takwaransa na Rasha Peter Szijjarto. REUTERS - Sergei Karpukhin
Talla

Ministan harkokin wajen Hungary Peter Szijjarto ya bayyana cewa, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov da kuma Andriy Yermak, mai taimakawa shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, kuma babu wanda ya yi watsi da tayin, sai dai lokacin da suka nema domin nazari akai.

A jiya Juma’a, fadar Kremlin ta ce a shirye shugaba Vladimir Putin yake ya aika da tawaga zuwa Belarus domin tattaunawa da Ukraine.

Shi kuwa ministan harkokin wajen Rashan Sergie Lavrov cewa ya yi a shirye suke su shiga tattauna amma bisa sharadin sai sojojin Ukraine sun ajiye makamansu, sai dai Amurka ta yi watsi da tayin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.