Isa ga babban shafi
Hungary-Ukraine

Hungary ta ki amincewa ayi amfani da samaniyarta wajen kai makamai Ukraine

Hungary ta ce ba za ta bai wa kasashen duniya damar kai wa Ukraine makaman da za ta yaki Rasha da su ta sararin samaniyar ta ba, bayan da kungiyar kasashen Turai ta ce za ta aikewa kasar makaman yaki.

Kasashen Turai na shirin amfani da sararin samaniyar Hungary wajen ratsawa Ukraine don kai mata taimakon kayakin yaki a yakin da ta ke da Rasha.
Kasashen Turai na shirin amfani da sararin samaniyar Hungary wajen ratsawa Ukraine don kai mata taimakon kayakin yaki a yakin da ta ke da Rasha. ASSOCIATED PRESS - ALEXANDER ZEMLIANICHENKO
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Peter Szijjarto ya bayyana haka, inda ya ke cewa ba za su bari ayi amfani da sararin kasar su wajen aikewa da makaman masu hadari ba.

Ministan ya ce sun dauki wannan mataki ne domin kare lafiyar jama’ar kasar su da ke gida da kuma wadanda ke zama a cikin kasar Ukraine.

Szijjarto ya ce ana iya amfani da safarar makaman wajen kai harin soji wanda ke iya yiwa jama’ar su illa.

Ministan ya ce babban abinda ke gaban su a wannan lokaci shi ne tabbatar da lafiyar kasar su da kuma jama’ar ta, saboda haka ba za su saka hannu a yakin da ke gudana a makociyar su ba.

Babban jami’in diflomasiyar kasashen Turai Josep Borrell ya ce za su bada euro miliyan 450 domin sayawa Ukraine makaman yakin da za a mika mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.