Isa ga babban shafi
Yemen

Dakarun Yemen na ci gaba da kutsawa Aden

Dakarun da ke biyayya ga Shugaban kasar Yemen Abedrabbo Mansur Hadi da ya tsere zuwa kasar Saudi Arabia sun yi nasarar kwace tashar jiragen sama a Aden daga hannun ‘Yan Tawayen Houthi, birni na biyu mafi girma a kasar.

Dakarun Gwamnati sun kwato tashar jiragen sama a Aden daga hannun ‘Yan Tawayen Huthi
Dakarun Gwamnati sun kwato tashar jiragen sama a Aden daga hannun ‘Yan Tawayen Huthi REUTERS/Stringer
Talla

Wannan ne karon farko da dakarun Gwamnati suka yunkuro tun bayan da Mayakan Huthi suka kwace garin Aden a watan Maris.

Dakarun sun tunkari mayakan ne tun a ranar lahadi abin da ya kawo karshen shirin tsagaita wutar da aka cim ma a cikin Azumi domin shigar kayan agaji ga mabukata.

Ya zuwa yanzu mutane sama da 3,200 aka kashe a tashin hankalin da ake ci gaba da yi a Yemen.

Saudiya da kawayenta dai har yanzu na ci gaba da luguden wuta da jiragen sama kan mayakan Huthi duk da Shugaban Amurka Barack Obama ya roki Sarki Salman na ya dakatar da kai hare haren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.