Al'ummar Iraqi na zanga-zangar rashin ruwan Famfo
Daruruwan al’ummar Iraqi ne ke gudanar da zanga-zangar matsalar ruwan sha a kudancin kasar na Basra, inda suka bukaci gwamnatin kasar ta gaggauta inganta lamari ko su fantsama a duk fadin kasar.
Wallafawa ranar:
Akalla mutane 500 ne suka fito a yau assabar, dauke da tutoci da aluna, inda sukayi cikan kwari a ofishin gwamnatin kasar, tare da bukatar inganta ruwan shansu da bashi da maraba da na gishiri.
A cewar daya daga cikin Jagororin zanga-zangar wanda kuma dalibi ne Ziyad Tareq yanzu lokaci ne da kowa ya san yan ci sa, don haka ya zama tilas gwamnati ta mayar da hankali domin biya musu bukatunsu, musamman abubuwan more rayuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu